Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Alibilad ta kasar Aljeriya ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da take gudanar da jawabi a gaban majalisar dattijan Faransa, Natalie Goli ta bayyana furucin Macron na nemen a yi wa addinin musulunci gyaran fsaka a kasar da cewa wuce gona da iri ne.
Ta ce addinin musulunci ba kayan wani mutum ne ko wani wasu ‘yan siyasa ba, a kan musulmin kasar ne kawa suke hakkin yin nazari dangane da abin da yake maslaha a gare su daidai da mahangar addininsu.
Emmanuel Macron dai ya bayyana bukatar ganin an gudanar da wasu sauye-sauye dangane da lamarin musulmi a kasar.